Home Labaru Martani: Ban Ce Sojojin Nijeriya Sangartattu Ba Ne – Buratai

Martani: Ban Ce Sojojin Nijeriya Sangartattu Ba Ne – Buratai

383
0

Shugaban rundunar dakarun sojin kasa na Nijeriya Janar Tukur Buratai, ya musanta rahotannin da ke cewa ya ce a yanzu Boko Haram na kara kaimin kai hare-hare ne saboda sojojin Nijeriya sun daina nuna kishin yakin kare martabar kasar su.

Janar Buratai ya ce an jirkita masa magana ta yadda aka isar da sakon sa a karkace ba kamar yadda ya furta da bakin sa ba.

Ya ce wasu bangarorin kafafen yada labarai ne su ka yi wa kalaman sa mummunar fahimta da nufin kulla ma shi sharri kawai.

Buratai ya bayyana haka ne, a wajen wani taron manema labarai da ya gabatar a Maiduguri, inda ya ce bai taba furta cewa sojoji sun sangarce ba su da kishin yakin kare martabar kasar su ba.