Home Labaru Siyasar Somaliya: ‘Yan Takarar Yankin Jubaland Sun Yi Ikirarin Lashe Zabe

Siyasar Somaliya: ‘Yan Takarar Yankin Jubaland Sun Yi Ikirarin Lashe Zabe

228
0

‘Yan takara biyu dake hamayya da juna a Somaliya, sun yi ikirarin lashe zaben yankin Jubaland, dake kudancin kasar mai amfana da wani mataki na kwarya-kwaryar cin gashin kai.

Tuni dai gwamnatin kasar ta Somaliya dake Mogadishu ta bayyana rashin amincewa da sakamakon zaben.

An dai yi ta dage zaben fidda shugaban yankin na Jubaland, dake da iyaka da kasar Kenya, sakamakon abin da masu sa ido suka daganta da gwagwarmayar karbe iko tsakanin yankin da kuma gwamnatin tsakiya ta Mogadishu.

Mahukuntan yankin Jubaland sun zargi gwamnatin Somalia da fadada ikon ta na tsige shugaba Ahmad Madobe, da sauya shi da wanda da ke yi mata biyayya.

A halin dake ciki, rahotanni sun ce rikici kan zaben na barazanar bazuwa zuwa sassan yankin na Jubaland da makwabtan sa, inda kasar Kenya ke marawa Madobe, baya yayin da Habasha ke bayan Mogadishu, mai kokarin kawar da Madobe daga kujerar mulki.

Sakamakon zaben yankin dai ya nuna cewar Madobe tsohon madugun yan tawaye, ya lashe kuri’u 56 cikin 74 da ‘yan majalisar yankin na Jubaland, suka jefa wanda zai tabbatar da shi shugaba na tsawon shekaru 4, yayinda Anab Muhammad Dahir, babbar abokiyar hamayyar sa kuma mace daya tilo da ta tsaya takara  da shi, ta samu kuri’u 17.