Home Labaru Kiwon Lafiya Bincike: Maleriya Na Ci Gaba Da Bijire Wa Magunguna

Bincike: Maleriya Na Ci Gaba Da Bijire Wa Magunguna

237
0

Wani sabon rahoton masana kimiyya ya ce aikin takaita yaduwar cutar zazzabin cizon sauro na cikin hatsari daga bijire wa magunguna barkatai da kwayar cutar ke yi.

Nazarin wanda ya bi diddigin kwayoyin cutukan da ke yada maleriya a Afirka ya gano siffofin kwayar halittar gado na kwayar cutar Plasmodium falciparum a yankuna daban-daban na Afirka.

Wannan ya hada da gadon dake sa kwayar cutar bijirewa magunguna birjik na yaki da maleriya.

Binciken ya yi karin haske kan yadda ake ta samun bijire wa magungunan cutar cizon sauro a yankuna daban-daban da kuma yadda halayyar bijirewar take matsa wa a fadin Afirka, lamarin da masana suka ce ya sanya cigaban da aka samu a baya cikin hatsari.

Cutar maleriya, matsala ce da ta addabi duniya, kuma nau’o’in kwayar cutar ta Plasmodium falciparum na bazuwa a yankin Kudu da sahara.

A tsakanin shekara ta 2000 zuwa 2015, yunkurin kawar da cutar ya yi nasarar ganin raguwar mace-macen zazzabin cizon sauro a fadin duniya daga mutum dubu 864 zuwa dubu 429 a shekara.