Home Labaru Aikin ‘Yan Sanda: Gwamnati Ta Samar Da Kayan Aiki Na Zamani Domin...

Aikin ‘Yan Sanda: Gwamnati Ta Samar Da Kayan Aiki Na Zamani Domin Sake Fasali

517
0
Shugaban kasa Muhammadu Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce a halin yanzu an sake fasalin tsarin rundunar ‘yan sandan Najeriya an kuma kara mata karfi tare da samar mata da kayan aiki irin na zamani ta yadda za ta su fuskanci kalubalen da ke gaban ta ba tare da wata fargaba ba.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari Da sarakunan Arewa

Shugaba Buhari, ya bayyana hakan ne yayin ganawar sa da sarakunan Arewa wadanda Mai Alfarma Sarkin Musulmi  Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar III, da Mai Martaba Sarkin Kano Dakta Muhammad Sanusi II, suka jagoran su zuwa fadar sa da ke birnin Abuja.

Bayanin hakan ya fito ne a cikin wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai Femi Adesina, ya rabawa manema labarai a Abuja.

Shugaban kasan ya ce gyaran da ake yi wa bangaren ‘yan sandan zai taimaka wajen kara bunkasa tsaro a kasa, kana Ma’aikatar kula ‘yan sanda ita aka dorawa alhakin gudanar sabbin tasare-tsaren, domin a samu ingantaccen tsaron da zai taimaka wajen kare lafiya da dukiyoyin al’umma.

Shugaba Buhari, ya kuma tabbatarwa ‘yan Najeriya kudirin gwamnatin sa na kare lafiya da dukiyoyin al’umma, sai ya yi kira ga al’umma da cewa kowa na da gudummowar da zai bayar wajen tabbatar da tsaron kasa.