Home Labaru Siyasar Sokoto: Kotun Daukaka Kara Ta Sake Tabbatar Da Zaben Tambuwal

Siyasar Sokoto: Kotun Daukaka Kara Ta Sake Tabbatar Da Zaben Tambuwal

439
0
Aminu Waziri Tambuwal, Gwamnan Jihar Sokoto

Kotun daukaka kara ta jihar Sokoto, ta sake tabbatar da zaben Aminu WaziriTambuwal a matsayin zababben gwamnan jihar Sokoto.

Kwamitin alkalai biyar a karkashin jagorancin mai shari’a Husseini Mukhtar, ya ce kotun daukaka kara ta amince da hukuncin kotun zabe, wadda a baya ta kori karar da jam’iyyar APC da dan takarar ta Ahmed Aliyu su ka shigar a kan Tambuwa.

Kotun, ta ce karar da aka daukaka ba ta da inganci, don haka ta kore ta.

Alkalai uku sun amince da hukuncin da mai shari’a Husseini Mukhtar ya zartar.

A ranar 16 ya watan Oktoba ne, Aliyu da jam’iyyar APC su ka daukaka kara a gaban kotun, inda su ke kalubalantar hukuncin da kotun zabe ta yanke a ranar 2 ga watan Oktoba na shekara ta 2019.