Home Labaru Kalaman Kiyayya: Gwamnoni Sun Ja Kunnen ’Yan Majalisar Dattawa

Kalaman Kiyayya: Gwamnoni Sun Ja Kunnen ’Yan Majalisar Dattawa

343
0

Kungiyar Gwamnonin Nijeriya, ta shawarci Majalisar Dattawa ta gudanar da zaman sauraren jin ra’ayin jama’a a kan kudirin kalaman kiyayya kafin su yi gaugawar maida shi ya zama doka.

Mataimakin Shugaban Kungiyar Aminu Tambuwal na Jihar Sokoto ya yi wannan kira, a lokacin da ya ke amsa tambayoyin manema labarai, bayan sun tashi daga taron da gwamnonin su ka halarta a Abuja.

Ya ce ko sau daya bai taba jin wani gwamna ya fito ya ce ya na goyon bayan kafa dokar hukuncin kisa a kan kalaman kiyayya ba.

Dangane da Dokar Karin Harajin kayayyaki da Shugaba Muhammadu Buhari ya aike wa Majalisar Dattawa don neman amincewar su, Tambuwal ya ce ya kamata ‘yan Nijeriya su rika fahimtar Buhari.

Ya ce gwamnoni su na goyon bayan abin da zai kara samar da kudaden shiga ga gwamnatin tarayya, da jihohi da kananan hukumomi, don haka su na rokon wadanda ba su fahimci dokar karin harajin ba su sake nazarin fahimtar lamarin sosai.

Leave a Reply