Home Labaru Siyasar Kogi: Sanata Dino Melaye Ya Sha Alwashin Zama Gwamna

Siyasar Kogi: Sanata Dino Melaye Ya Sha Alwashin Zama Gwamna

400
0

Dan majalisar dattawa Sanata Dino Melaye, ya ce za a zabe shi a matsayin gwamnan jihar Kogi a zaben da zai gudana a cikin watan Nuwamba na shekara ta 2019.

Idan dai za a iya tunawa, kwanakin baya ne Sanatan ya kaddamar da kudirin sa na neman kujerar gwamnan jihar Kogi a karkashin jam’iyyar PDP.

Dan majalisar, ya dukufa wajen yakin neman da manyan hotunan sa da ya ke dorawa a shafukan sadarwa na yanar gizo, yayin da ya ke jadada nasarorin da ya samu a jihar Kogi.

Jam’iyyar PDP dai na ci-gaba da kyautata zaton samun nasara a zaben gwamnan jihar Kogi da za a gudanar ranar 2 ga watan Nuwamba na shekara ta 2019.

Leave a Reply