Home Labaru Dubu Ta Cika: Sojoji Sun Kama Shugaban Masu Garkuwa Da Mutane A...

Dubu Ta Cika: Sojoji Sun Kama Shugaban Masu Garkuwa Da Mutane A Katsina

758
0

Dakarun rundunar soji ta 17 a karkashin atisayen ‘Harbin Kunama III’, ta samu nasarar kama wani shugaban ‘yan ta’adda mai suna Mallam Bawa Gwamna da yaran sa 20 a jihar Katsina.

Gwamna da yaran sa dai sun yi kaurin suna wajen sace mutane tare da yin garkuwa da su a yankin kananan hukumomin Batsari da Safana da Jibia, inda dakarun soji su ka kama su yayin wani atisaye a cikin watan Yuni na shekara ta 2019.

Da ya ke tabbatar da kama ‘yan ta’addan, mukaddashin daraktan hulda da jama’a da yada labarai na rundunar soji Kanal Sagir Musa, ya ce sun kama wasu daga cikin su ne yayin da su ke kan aikata ta’addanci, wasu kuma an kama su ne ta hanyar samun sahihan bayanan sirri.

Ya ce ya kamata su sanar da jama’a cewa, ‘yan ta’addan da su ka kama da kuma wasu da su ka tsere, su ne su ka addabi kananan hukumomin Batsari da Safana da Jibia da ayyukan ta’addanci.

A karshe ya ce ‘yan bindgar sun amsa da bakin su, cewa su na daga cikin ‘yan bindigar da ke satar shanu tare da yin garkuwa da mutane a yankin kananan hukumomin.