A ranar lahadin nan ne, mutanen kasar Kazakhstan ke zaben shugaban kasa, bayan Shugaban kasar mai ci Noursoultan Nazarbaiev ya yi murabus a watan Maris sanadiyar rashin lafiya.
Akalla mutane milyan 10 ne hukumar zabe ta kasar ta bayyana su matsayin wandanda su ka yi rajista, sai dai ana hasashen daya daga cikin mukarraban Noursoultan Nazarbaiev kuma shugaban rikon kwarya Kassym Jomart Tokaiev zai lashe wannan zabe.
Kassym Jomart Tokaiev mai shekaru 66, zai fafata da wasu ‘yan takara guda shida, wadanda ba su da wata kima a idanun ‘yan kasar ta Kazakhstan.