Home Labaru Dokar Wa’azi: Ra’ayoyin Can Da Jama’atu Sun Sha Bamban A Jihar Kaduna

Dokar Wa’azi: Ra’ayoyin Can Da Jama’atu Sun Sha Bamban A Jihar Kaduna

652
0

Kungiyoyin addinai a jihar Kaduna sun nuna mabambantan ra’ayoyi game da sabuwar dokar gudanar da harkokin addinin da za a kawo.

Daya daga cikin manyan malaman addinin Kirista Mista Sunny Akanni, yay i barazanar maka majalisar dokoki ta jihar Kaduna kotu saboda amincewa da wannan kudiri.

Akanni ya ce majalisar jihar Kaduna ta saba wa umarnin kotu na sanya hannu a kan wannan doka da za ta yi wa sha’anin addini garambawul, alhalin maganar ta na gaban kotu amma majalisar ba ta yi la’akari da hakan ba.

Kungiyar kiristoci ta Nijeriya CAN, ta ce za ta duba wannan kudiri, inda ta nuna cewa ta na da ja a kan wannan doka da ake shirin kawowa kamar yadda Shugaban kiristoci na jihar Kaduna Joseph Hayab ya bayyana.

A nata bangaren kuma, kungiyar Jama’atu Nasril Islam ta yi farin ciki da jin labarin wannan doka, inda Sakataren ta Yusuf Adamu ya ce babu wata matsala tattare da wannan kudiri da aka kawo, domin duk wanda zai yi wa’azi yadda ya dace bai kamata ya ji tsoron dokar da za a kawo ba.

Leave a Reply