Home Labaru Siyasar Kenya: William Ruto Na Son Zama Shugaban Kasa

Siyasar Kenya: William Ruto Na Son Zama Shugaban Kasa

61
0
kenyan_deputy_president_william_ruto

Mataimakin shugaban kasar Kenya William Ruto ya bulo da salon neman amincewar masu kada kuri’a a zaben da za a yi a kasar a shekara mai zuwa inda yake amfani da salon tura wul baro da kuma jaddada cewa ya taba tallan kaji, duk dai domin ya nuna cewa takarar zaben ta rabu ne tsakanin masu fafutukar neman na kan su da kuma ‘yan na-gada.

A kasar Kenya, kamar yadda sunan ya nuna, masu fafutukar neman na kansu na nufin – musamman matasa – wadanda suke fafutukar neman kudi a yanayin tattalin arzikin da ke da wahalar sha’ani.

A gefe guda, ‘yan na-gada na nufin mutanen da suka fito daga attajiran iyaye wadanda suka mamaye harkokin siyasa – da kuma tattalin arziki- tun da kasar ta samu ‘yancin kai daga Birtaniya a shekarun 1960.

An sanya Shugaba Uhuru Kenyatta da dan siyasar hamayya Raila Odinga a rukunin ‘yan na-gaba.

Uhuru Kenyatta ɗa ne ga shugaban Kenya na farko, yayin da shi kuma Raila Odinga, ɗa ne ga mataimakin shugaban kasar na farko, ko da yake Mr Odinga ne ɗan siyasar Kenya da ya fi daɗewa a kurkuku saboda siyasa kuma shi ne ya jagoranci fafutikar kawo sauyi a harkokin siyasar kasar.

Mr Ruto, mai shekara 54, shi ne ya kirkiri kalmar “masu fafutukar neman na kansu” a matsayinsa na dan siyasa na cike da kazar-kazar da buri mai girma.