Home Labaru Cimma Matsaya: Ronaldo Zai Koma Manchester United Da Taka Leda

Cimma Matsaya: Ronaldo Zai Koma Manchester United Da Taka Leda

52
0
Ronaldo Manchester

Manchester United ta ce ta cimma matsaya da Juventus domin sayen dan kwallon Portugal Cristiano Ronaldo.

A wani saƙo da Manchester United ta wallafa, ta ce maraba da zuwa gida Ronaldo, wadda wannan alama ce da ke nuna cewa Ronaldo zai koma kulob ɗin.

Manchester United ta ce kammala cinikin ɗan wasan da ya lashe Ballon d’Or sau biyar ya ta’allaƙa ne da batun abin ɗan wasan yake so da kuma batun samun biza da kuma lafiyar sa.

Ronaldo ya ci ƙwallo 118 a wasanni 292 da ya buga a lokacin da yake Old Trafford kafin daga baya ya koma Real Madrid.