Home Labaru Kiwon Lafiya Mai Dokar Bacci: Jami’In China Mai Yaki Da Cin Hanci Da...

Mai Dokar Bacci: Jami’In China Mai Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa Ya Karbi Na Goro

48
0
Chinese Flag

Wani babban jami’in gwamnatin China da a baya ke jagorantar yaki da cin hanci da rashawa – shi ma an kama shi da laifin karbar cin hanci.

Dong Hong ya gaya wa kotun da ta yi ma sa shari’a cewa ya karbi cin hancin sama da dalar Amurka miliyan saba’in ciin shekara ashirin da su ka gabata.

An kuma tuhume shi da gudanar da rayuwar da ta fi karfin kudaden da yake samu, inda aka same shi yana ziyartar kulob-kulob din da sai hamshakan masu hali ke iya shiga.

A baya Mista Hong ya kasance mataimakin babbar hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta China.

Ya kuma taba zama na hannun daman mataimakin shugaban kasar, Wang Qishan.

Sai dai ba kasafai akan tuhumi jami’ai makusantan shugabannin China da laifukan rashawa ba.