Kotun sauraren kararrakin zaben gwamna da ke zama a Birnin Kebbi, ta yi watsi da karar da jam’iyyar PDP ta shigar ta na kalubalantar nasarar jam’iyyar APC da dan takarar ta Atiku Bagudu a zaben shekara ta 2019.
Da ta ke yanke hukunci, mai shari’a Amina Adamu Aliyu ta tabbatar da cewa, karar da PDP ta shigar ba ta da muhimman hujjojin da ake bukata, wanda zai iya bayyana zaben a matsayin wanda ke cike da magudi kamar yadda dan takarar ta Sanata Isa Galaudu ya yi ikirari.
Mai shari’a Amina Aliyu, ta ce an soke shari’ar saboda rashin inganci.
Da
ya ke tsokaci game da hukuncin, lauyan Bagudu da jam’iyyar APC Yakubu Maikiyau,
ya ce hukuncin da alkalan kotun su ka yanke ya na kan ka’ida, ya na mai cewa, idan
har PDP ba ta gamsu da hukuncin ba ta na iya garzayawa kotun daukaka kara.
You must log in to post a comment.