Home Labaru Babu Tabbacin An Yi Amfani Da Alburusai A Kan ‘Yan Shi’a -‘Yan...

Babu Tabbacin An Yi Amfani Da Alburusai A Kan ‘Yan Shi’a -‘Yan Sanda

365
0

Rundunar ‘yan sandan Nijeriya, ta ce ba za ta iya tabbatar da ko an yi amfani da alburusai akan wasu ‘yan Shi’a da su ka yi zanga-zanga a Abuja ba.

Da farko dai an ruwaito cewa, rundunar ‘yan sandan ta harba barkonon tsohuwa da alburusai domin tarwatsa ‘yan Shi’ar da ke tattaki zuwa sakatariyar tarayya ta Abuja.

Zanga-zangar ‘yan shi’an da aka fara cikin lumana dai ta koma rikici, yayin da ‘yan sanda su ka datse hanyar sakatariyar sannan su ka harba barkonon tsohuwa domin tarwatsa su.

Karanata Labaru masu Alaka: Kawunan ‘Yan Majalisar Wakilai Sun Rarraba

Kakakin rundunar ‘yan sanda na birnin tarayya Anjuguri Manzah, ya ce rundunar ba za ta iya tabbatar da ko an an yi amfani da alburusai a kan ‘yan shi’ar ba, bayan mai Magana da yawun ‘yan shi’ar Abdullahi Musa ya yi zargin cewa, ‘yan sanda sun yi amfani da alburusai domin tarwatsa mutanen su a sakatriyar.