Home Labaru Abin Da Ya Sa ‘Yan Arewa Ke Hakuri Da Shugaba Buhari –...

Abin Da Ya Sa ‘Yan Arewa Ke Hakuri Da Shugaba Buhari – Shehu Sani

618
0

Tsohon dan majalisar dattawa Sanata Shehu Sani, ‘ya ce al’ummar Arewacin Nijeriya su na hakuri da salon mulkin Shugaba Buhari ne saboda daga yankin ya fito.

Shehu Sani ya bayyana haka ne, a wajen wani taro da aka gudanar a Kaduna, inda ya ce yankin Arewa bai dauki wani kwakwaran mataki a kan shugaba Buhari ba duk da kashe-kashe da asarar dukiyoyin da ake yi a yankin.

Sanatan, ya kuma koka a kan koma-bayan ilimi da tsananin talaucin da ‘yan Arewa ke fama da shi, ya na mai yin kira ga shugaba Muhammadu Buhari ya gaggauta daukar matakin da ya dace.

Shehu Sani ya kara da cewa, ‘yan Arewa su na hakuri da gwamnatin APC ne a yanzu saboda Buhari ke mulki kuma shi ma dan arewa ne kamar su.