Home Labaru Kungiyar Amotekun: Gwamnati Ta Cimma Matsaya Da Gwamnoni

Kungiyar Amotekun: Gwamnati Ta Cimma Matsaya Da Gwamnoni

512
0
Kungiyar Amotekun: Gwamnati Ta Cimma Matsaya Da Gwamnoni
Kungiyar Amotekun: Gwamnati Ta Cimma Matsaya Da Gwamnoni

Gwamnatin tarayya tace ta kulla yarjejeniya da gwamnonin jihohin yammacin Najeriya 6 kan yadda shirin su na kafa rundunar tsaron da aka yiwa lakabi da Amotekun zai yi aiki ba tare da saba dokokin kasa  ba.

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, ya bayyana haka, bayan wani taro da yayi da gwamnonin jihohin dake yankin tare da ministan shari’a Abubakar Malami, da kuma Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya Muhammadu Adamu.

Mai magana da yawun mataimakin shugaban kasa Laolu Akande, ya ce gwamnonin ne suka bukaci ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari kan lamarin, amma sai ya sanya mataimakin sa Osinbajo ya wakilce shi.

Akande yace an samu fahimtar juna tsakanin bangarorin dangane da kafa rundunar, yayin da suka amince su sanya ta a karkashin shirin gwamnatin tarayya na samar da tsaron al’umma da kuma yin dokokin da suka dace. Gwamnan jihar Ondo Rotimi Akeredolu, da yayi magana a madadin gwamnonin ya tabbatar da matsayin mataimakin shugaban kasar da kuma aniyar su na ganin an warware matsalar ta fannin siyasa da kuma dokar kasa.