Home Labaru Siyasar Faransa: An Jefi Shugaba Macron Da Kwai A Bainar Jama’a

Siyasar Faransa: An Jefi Shugaba Macron Da Kwai A Bainar Jama’a

15
0

Wani mutum ya jefi Shugaban Kasar Faransa, Emmanuel Macron da kwai cikin jama’a, a wata kasuwar baje koli dake birnin Lyon na kasar.

Macron yana tsaka da gaisawa da mahalarta baje-kolin a karkashin rumfar wani otal ne aka jefe shi da kwai, inda ya same shi a kafada.
Mutumin ya yi jifar ne a daidai lokacin da Macron ke gaisawa da mutanen da ke karkashin rumfar, suna jinjina masa bisa tallafin da gwamnatinsa ta ba wa bangaren otal na kasar domin rage musu radadin annobar COVID-19.
Sai dai kuma kwan da aka jefi Macron da shi bai fashe a jikinsa ba, kuma nan take jami’an tsaro suka kama mutumin da yayi jifan.
Da yake magana kan jifar sa da aka yi, shugaban na Faransa ya ce, “Idan har (mutumin) yana da abin da yake son ya fada masa to a shirye yake ya saurare shi.
Wannan shine karo na uku da ake samun masu cin mutuncin Macron a bainar jama’a.
Idan ba a manta ba, a watan Yuni wani mutum ya mari shugaban kasar a bainar jama’a a lokacin shugaban yake musabaha da shi a yankin Valence.
Kafin nan a 2017 an jefi Macron da kwai a lokacin yakin neman zabe a birnin Paris na kasar.