Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa kasar Habasha domin halartar bikin rantsar da firaminista Abiy Ahmed a sabon wa’adi na biyu da zai gudana a yau Litinin.
Wata sanarwa da fadar shugaban kasa ta fitar a ranar Asabar ta ce, shugaba Buhari na daga cikin manyan bakin da za su yi jawabi a bikin rantsar da Abiy Ahmed.
Daga cikin wadanda suka rufa wa shugaba Buhari baya a cewar sanarwar wacce Femi Adesina ya fitar, akwai ministan harkokin wajen Geoffrey Onyeama, da babban daraktan hukumar tattara bayanan sirri Ambasada Ahmed Rufai Abubakar.
A ranar Talata ne dai ake sa ran shugaba Buhari zai dawo gida Najeriya.
You must log in to post a comment.