Home Labaru Siyasar Edo: Obasrki Ya Kammala Shirin Barin Jam’iyyar APC – Oshiomole

Siyasar Edo: Obasrki Ya Kammala Shirin Barin Jam’iyyar APC – Oshiomole

366
0
Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Adams Oshiomole
Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Adams Oshiomole

Shugaban jam’iyyar APC na kasa Adams Oshiomhole, ya ce gwamnan jihar Edo Godwin Obaseki ya kammala shirye-shiryen ficewa daga jam’iyyar APC.

Oshiomhole ya bayyana haka ne, ta bakin mai magana da yawun sa Simon Ebegbulem, inda ya ce gwamnan ya na kokarin raba kan ‘yan jam’iyyar ne kafin ya tsallake daga cikin ta.

Ya ce su na da sahihin labarin cewa, gwamnan ya na shirin fasa jam’iyyar APC, kuma da zarar ya cimma wannan manufa zai ya fice daga jam’iyyar zuwa wata, don haka ne ya fara yin gaban kan sa a duk sha’anin mulki ba tare da duba ga tanadin doka ba.

Oshiomole ya kuma yi kira ga gwamnan da ya daina bata ma shi suna, maimakon haka, ya ce ya maida hankalin sa wajen tafiyar da sha’anin mulki, wanda shi ne dalilin da ya sa aka zabe shi.