Home Labaru Rundunar Soji Ta Kallubalanci Ndume Kan Ikirarin Kisan Sojoji 847

Rundunar Soji Ta Kallubalanci Ndume Kan Ikirarin Kisan Sojoji 847

261
0
Sanata Ali Ndume

Rundunar Sojojin Nijeriya, ta bukaci Sanata Ali Ndume da kwamitin kula da harkokin soji na majalisar dattawa,  su gabatar da hujojjin da ke nuna cewa ‘yan ta’addan Boko Haram sun kashe sojojin Nijeriya sama da 840.

Sanatan Ndume dai ya ce, daga shekara ta 2013 zuwa yanzu, a kalla sojoji 840 ne aka birne a makabartar sojoji da ke Maiduguri na jihar Borno, ikirarin da mai magana da yawun rundunar sojin Nijeriya Sagir Musa ya karyata.

Sagir Musa ya ce, idan abin da Ndume ya ce kenan sai ya gabatar da hujojjin da ya dogara da su.

Idan dai ba a manta ba, a wani rahoton da jaridar Wall Street Journal ta wallafa a watan Augusta, ta ce sama da sojojin Nijeriya 1,000 ne da aka kashe a fagen daga, aka kuma birne cikin sirri a Maiduguri.