Home Labaru Gargadi: Gwamnan Bauchi Ya Yi Barazanar Tsige Duk Sarkin Da Ya Hada...

Gargadi: Gwamnan Bauchi Ya Yi Barazanar Tsige Duk Sarkin Da Ya Hada Kai Da ‘Yan Ta’adda

582
0
Bala Mohammed, Gwamnar Jihar Bauchi
Bala Mohammed, Gwamnar Jihar Bauchi

Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi, ya ce zai tsige duk wani basaraken jihar da aka samu da hada kai da yan ta’adda.

Bala Mohammed ya yi gargadin nec, yayin da ya karbi bakuncin ‘yan majalisar sarakunan jihar Bauchi a karkashin jagoancin Sarkin Bauchi Alhaji Rilawanu Sulaiman Adamu.

Gwamnan ya yi korafin cewa, ‘yan fashi da makami da masu garkuwa da mutane da aka fatattaka daga sauran jihohi su na shiga jihar Bauchi domin haddasa rashin zaman lafiya.

A karshe ya ce gwamnatin sa za ta yi aiki tare da masarautun gargajiya da sauran hukumomi masu amfani domin tabbatar da ganin ayyukan ta’addanci sun zama tarihi a jihar Bauchi.