Home Labaru Siyasar Ebonyi: Kotu Ta Tsige Dan Majalisar PDP Ta Ba Dan Takarar...

Siyasar Ebonyi: Kotu Ta Tsige Dan Majalisar PDP Ta Ba Dan Takarar APC

335
0

Kotun sauraren kararrakin zaben majalisar dokoki ta tarayya da ke zama a birnin Abakaliki na jihar Ebonyi, ta soke nasarar zaben dan majalisa mai wakiltar mazabar Ikwo da Ezza ta kudu Lazarus Ogbee.

Hukumar zabe mai zaman kan ta ta kasa INEC, ta kaddamar da Ogbee a matsayin wanda ya lashe zaben da aka gudanar a ranar 23 ga watan Satumba, yayin da Kotu zaben a karkashin jagorancin mai shari’a Sika Henry Aprioku ta kaddamar da abokin adawar sa Chinedu Ogar na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben.

Ogar dai ya shigar da kara kotu ne domin kalubalantar sakamakon zaben, inda yayi ikirarin cewa hukumar zabe ta rage yawan kuri’un sa don ganin Ogbee ya yi nasara.

Leave a Reply