Home Labaru Rashin Sadaki: Budurwa Ta Cinna Wa Kan Ta Wuta A Jihar Zamfara

Rashin Sadaki: Budurwa Ta Cinna Wa Kan Ta Wuta A Jihar Zamfara

1321
0

Wata budurwa ‘yar shekaru 17 ta dauki wani mummunan mataki a kan ta, ta hanyar banka wa kan ta wuta bayan ta bulbula wa jikin ta man fetur, saboda saurayin da ta ke soyayya da shi ya gaza biyan sadakin auren ta.

Yarinyar mai suna A’isha da ta ke zaune a unguwar Albarkawa a cikin garin Gusau tare da iyayen ta, ta yi kokarin kashe kan ta ne sakamakon tsananin talaucin da ke damun saurayin ta Umar, lamarin da ya kai ga har ba zai iya biyan Naira dubu 17,000 a matsayin sadakin auren ta.

Wata majiya ta ce, iyayen A’isha sun gayyaci Umar domin ya fito a fara shirye-shiryen aure, amma ya ce masu ba zai iya fitowa ba sakamakon bay a da Naira 17,000 da su ka yanka masa a matsayin sadaki.

Majiyar ta ce, daga nan ne A’isha ta dauki wani galan cike da man fetur ta wanke jikin ta da shi, sannan ta kyasta ashana ta fara ci da wuta.

Yanzu haka dai A’isha ta na samun kulawa da magungunan gargajiya a gida, sai dai kakakin ‘yan sanda na jihar Zamfara Muhammadu Shehu ya bayyana rashin masaniya game da aukuwar lamarin.