Home Labaru Bugun-Kirji: Ni Zan Sake Lashe Zaben Gwamnan Jihar Kogi – Yahaya Bello

Bugun-Kirji: Ni Zan Sake Lashe Zaben Gwamnan Jihar Kogi – Yahaya Bello

318
0
Yahaya Bello, Gwamnan Jihar Kogi

Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello, ya ce ya kammala duk wasu shirye-shiryen tabbatar da samun nasara a zaben gwamnan jihar da za a yi ranar 16 ga watan Nuwamba na shekara ta 2019.

Yahaya Bello ya bayyana wa manema labarai haka ne, jim kadan bayan ganawar sa da shugaba Muhammadu Buhari da shugaban jam’iyyar APC Adams Oshiomhole a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Gwamnan ya ce ya kammala duk wasu shirye-shiryen tabbatar da nasarar sa tun gabanin zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya da aka gudanar a watan Fabrairun da ya gabata.

Yahaya Bello ya cigaba da cewa, kwazo da kuma rawar da ya taka a kujerar mulki manuniya ce ta nasara, don kuwa ya zuwa yanzu al’ummar jihar Kogi sun shirya domin sake yi ma shi ruwan kuri’u a zaben na watan jibi.