Home Labaru Siyasar Burtaniya: Theresa May Ta Yi Murabus A Yau Juma’a

Siyasar Burtaniya: Theresa May Ta Yi Murabus A Yau Juma’a

354
0

Firaministar Birtaniya Theresa May ta sanar da yin murabus daga kujerar ta bayan ta gaza gabatar da yarjejeniyar ficewa daga kungiyar tarayyar turai, inda ta kara da cewa ta yi iya bakin kokarin ta sannan tana fatan wanda zai gaje ta zai yi nasara a inda ta gaza.

Theresa May ta yi fitar da wannan sanarwar ne a yau juma’a 24 ga watan Mayu, inda ta yi amfani da damar wajen jero nasarorin da ta samar a kasar.

Cikin kuka mai taba zuciya, ta ce ita ce mace ta biyu da ta rike mukamin Firaminista, amma ba ita zata zama ta karshe ba.

Yin murabus din da na zuwa ne, a dai dai lokacin da al’ummar kasar ke kada kuri’a a zaben Majalisar Tarayyar Turai. kuma wani hasashe ya nuna cewa, bangaren masu ra’ayin ci gaba da zaman Birtaniyar a tarayyar turai zai samu gagarumin rinjaye.

Leave a Reply