Home Labaru Rantsar Da Buhari: Gwamna Masari Ya Soke Bikin Ranar 29 Ga Watan...

Rantsar Da Buhari: Gwamna Masari Ya Soke Bikin Ranar 29 Ga Watan Mayu A Katsina

517
0

Gwamnatin jihar Katsina ta soke duk wasu shagulgula da za a gudanar a jihar domin murnar bikin ranar 29 ga watan Mayu, sai dai rantsar da gwamna da mataimakin sa kawai, domin nuna alhini da mutuwar wadanda ‘yan bindiga suka kashe a wannan makon a jihar.

Sakataren gwamnatin jihar Mustapha Inuwa ya ce an yanke hukuncin yin haka ne bayan wasu munanan hare-hare da ‘yan bindiga suka kai a wasu yankunan jihar.

A cewar sa hare-haren sun yi sanadiyar mutuwar mutane da dama. sannan sun jikkata wasu dama yayin da wasu suka zama marasa gata.

Yayin da yake rokon mutanen jihar da su kwantar da hankalin su, Inuwa ya bukace su da su jajirce wajen addu’o’i, musamman a wadannan ranakun karshe na Ramadana, don samun zaman lafiya mai dorewa a jihar.

Leave a Reply