Home Labaru Afghanistan: Taliban Ta Yi Bikin Ficewar Amurka

Afghanistan: Taliban Ta Yi Bikin Ficewar Amurka

78
0
Taliban

Mayakan Taliban sun yi bikin murnar karbe iko da gwamnatin Afghanistan baki daya bayan Amurka ta kammala ficewa daga kasar a yau Talata, inda suka yi ta harbe-haren bindiga a sararin samaniya.

A hukumance, Amurka ta kawo karshen yaki mafi dadewa da ta yi tarihi, domin kuwa ta shafe kimanin shekaru 20 tana fafatawa da ‘yan ta’adda a Afghanistan.

Dakarun Amurka sun fice daga filin jiragen sama na birnin Kabul, inda suka shafe tsawon kwanaki suna sanya ido kan kwashe jama’ar da ke son ficewa daga Afghanistan.

Sama da mutane dubu 123 ne aka kwashe daga kasar ta Afghanistan domin tsoron mulkin zalinci na Taliban.

Jim kadan da ficewar sojojin Amurka, mayakan na Taliban sun mamaye harabar filin jiragen sama na birnin Kabul tare da harbe-harben bindigogi domin nuna murna.