Home Labaru Shugabancin NISTF: Kungiyar Kwadago Ta Fara Zanga-Zangar Game – Gari

Shugabancin NISTF: Kungiyar Kwadago Ta Fara Zanga-Zangar Game – Gari

339
0

Kungiyar Kwadago ta Kasa NLC, ta bada sanarwar fara yajin aiki tun daga ranar Litinin 13 ga watan Mayu na shekara ta 2019.

Yajin aikin dai ya bijiro ne sanadiyyar rikicin da kungiyar ke yi da Ministan Kwadago a kan shugabancin Hukumar Gudanarwa ta asusun inganta rayuwar al’umma.

Kungiyar Kwadago da Ma’aikatar Kwadago dai kowa ya na goyon bayan wani bangare daban na Shugabancin hukumar.

NLC ta ce yanke hukuncin fara yajin aikin ya zama tilas, saboda matakin da Ministan Kwadago Chris Ngige ya dauka. Kungiyar NLC ta ce, su na mmakin yadda za a tura Frank Kokori zuwa Cibiyar Horar da Ma’aikatan Kwadago a Ilorin, bayan daga farko shi ne aka ba shugabancin Hukumar Gudanarwa  ta asusun inganta rayuwar al’umma NISTF.

Leave a Reply