Wani lauya kuma kwararre a fannin fallasa yadda ake satar kudade George Uboh, ya kalubalanci kokarin da Gwamnatin Tarayya ke yi na sake nada Godwin Emiefele a matsayin gwamnan Babban Bankin Nijeriya CBN karo na biyu.
Idan dai majalisa ta amince da tayin da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi mata na neman Emiefele ya cigaba da rike shugabancin CBN, zai sake shafe wasu shekaru hudu kenan a matsayin sa na Gwamnan bankin.
Lauya Uboh, wanda wakili ne na zakulo inda ake karkatar da kudade, ya nemi kotu kada ta amince a sake nada Emiefele a matsayin gwamnan babban bankin Nijeriya CBN.A cikin dalilan da ya gabatar wa Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, Uboh ya ce ba zai yiwu Gwamnatin Tarayya ta aika da sunan Godwin Emiefele ga Majalisar Dattawa cewa ta sake amincewa da shi ba, domin akwai kara a gaban kotu da ke kalubalantar sake nada shi.