Home Labaru Shugabancin Majalisa: ‘Yan Majalisa 164 Na Tare Da Gbajabiamila

Shugabancin Majalisa: ‘Yan Majalisa 164 Na Tare Da Gbajabiamila

219
0

‘Yan majalisa 164 ne ke goyon bayan Femi Gbajabiamila a cikin majalisar wakilai da aka zaba a jam’iyyar APC.
Wadanda suka yi wannan zaben sun ce ba za su kalubalanci Shugaban kasa Muhammadu Buhari ba, ka na ba za su tsoki jam’iyyar APC ba, akan zabin da suka yi.
Jam’iyyar APC ta amince da cewa duk yunkurin da aka yi domin gabatar da wanda zai yi jagoranci a yi zabe gwamnatin shugaba Buhari ta na tare da shi.
Jam’iyyar ta bayyana hakan ne a wajen taron cin abinci wanda ya gudana a fadar shugaban kasa dake Abuja, inda aka fitar da wata sanarwa da Mista Tunji Ojo da kuma Darakta Janar Dunusun Chamberlain, sanyawa hannu, inda suka ce matsayin shugaban kasa a kan wannan abu shi ne mutane su zabi abinda suke so.
Sanarwan ta ce suna kira ga dukkannin ‘yan jam’iyar APC su girmama jam’iyya, sannan su yi amfani da duk wani mataki da ta yanke akan wannan lamarin.

Leave a Reply