Home Labaru Majalisa: Ba Mu Yarda Da Zaben Gbajabiamila Ba- Matasan Arewa

Majalisa: Ba Mu Yarda Da Zaben Gbajabiamila Ba- Matasan Arewa

222
0

Kungiyar Matasan Arewa ta yi watsi da zabin jam’iyyar APC na tsayar da Femi Gbajabiamila a matsayin kakakin majalisar wakilai.
Shugaban kungiyar Mohammed Sani Kabir, ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya sanyawa hannu, ya ce yarjejeniyar ta sabawa yankin arewacin Najeriya a zaben shugaban kasa da za a yi na shekara ta 2023.
Mohammed Sani, ya ce kungiyar na goyon bayan ‘yan majalisar wakilai, wadanda suka nuna rashin goyon bayan su ga zabin da jam’iyyar ta yi, saboda zabin da jam’iyyar APC ta yi ba zai amfanawa yankin arewa komai ba.
Kungiyar ta bukaci shugabannin jam’iyyar APC su kyale ‘yan majalisu su zabi wanda zai shugabance su, sannan kuma ta bukaci ‘yan majalisu su lura wajen zaben shugaba wanda zai kawo ci gaba a Najeriya.
Daga karshe kungiyar ta yi kira ga jam’iyyar APC ta kyale ‘yan majalisu su zabi wanda suke so ya shugabance su, ba wai dole sai Ahmed Tinubu ko kuma Adams Oshiomhole sun tilastawa mutane Ahmad Lawan da Femi Gbajabiamila a majalisa ba.