Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana takaicinsa a akan rikicin da ya addabi kabilar Jukun da Tibi a jihar Taraba da kuma na Fulani da Genjon da kabilar Bachama na jihar Adamawa.
Mai magana da yawun shugaban kasa Garba Shehu, ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Abuja.
Ya ce, tashin hankali da zubar da jini ta kowanne hanya abu ne da ba za a amince da shi ba, musamman a wannan lokacin da ake bukukuwan Ista a Najeriya, duk da darussa da wannan lokacin ke koyarwa na zaman lafiya ba tare da nuna bambamci ba.
Buhari, ya ce tashin hankali ba zai taba zama hanyar maganin rashin fahintar da ake fuskanta a tsakanin mutane ba, inda ya yi kiran kawo karshen rikicin.
Ya ce, gwamnati za ta nemi a tattauna a tsakanin dukkannin masu ruwa da tsaki domin gano musabbabin rikicin da nufin kawo karshen rikicin gaba daya.
Daga karshe shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci Malaman addini su gaggauta samar da hadin kai da zama lafiya a tsakanin bangarorin dake tashin hankali a jihohin Filato da Kaduna da Taraba da kuma Adamawa.
You must log in to post a comment.