Home Labaru Siyasa Shugabancin Majalisa: PDP Na Shirin Mara Wa Sanata Danjuma Goje Baya

Shugabancin Majalisa: PDP Na Shirin Mara Wa Sanata Danjuma Goje Baya

187
0
Danjuma Goje, Tsohon Gwamnan Jihar Gombe

Yayin da fafutukar neman kujerar shugaban majalisar dattawa ke kara zafi, jam’iyar PDP ta na kokarin hada kai da daya daga cikin masu neman shugabancin majalisar.

Jam’iyar ta PDP dai ta na da niyyar mara wa shugaban kwamitin kasafi na majalisar dattawa Sanata Danjuma Goje baya a matsayin shugaban majalisar da kuma Sanata Ike Ekweremadu a matsayin mataimaki.

Sai dai wasu ‘yan jam’iyar PDP su na tunanin ko dai Ali Ndume da Ekweremadu ko kuma Abdullahi Adamu da Ekweremadu a matsayin ‘yan takarar da za su goya wa baya.

Akasarin zababbun ‘yan majilasar dattawa na jam’iyar PDP musamman wadanda ke matukar biyayya ga Sanata Bukola Saraki sun nuna rashin amincewar su da Sanata Abdullahi Adamu da Ali Ndume.

Saraki da wasu jiga-jigan jam’iyar PDP dai sun fi son Sanata Goje, wanda ya kasance babba ne a jam’iyar PDP kafin ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC.