Helkwatar hukumar soji ta kasa, ta ce sabon karin albashin ma’aikata da gwamnatin tarayya ta kaddamar bai hada da ma’aikatan hukumar sojin Nijeriya ba.
Hukumar ta maida martani ne ga wasu takardun karya da ke yawo a kafar sadarwa ta zamani dangane da lamarin.
Ta ce ta na so ta bayyana wa al’umma cewa, wadannan takardu na karya ne ba su da tushe, kuma ana yada su ne domin a kawo rudani ga jami’an hukumar soji kamar yadda Kanar Onyema Nwachukwu ya bayyana.
Nwachukwu ya ce, hukumar ba ta ji dadin ganin takardun karyar da su ke yawo a kafar sada zumunta ba, wadanda ke nuna sabon tsarin albashin ma’aikata da zai fara aiki a watan Mayu na shekara ta 2019.
Idan dai ba a manta ba, shugaba Muhammadu Buhari ya sanya hannu a kan dokar karin albashin ma’aikata, inda za a rika biyan su naira dubu 30 a kowane wata.
A karshe ya ce, ya na da matukar muhimmanci mutane su gane cewa hukumar soji ba ta kara wa ma’aikatan ta albashi ba.