Home Labaru Kashe-Ashe: An Bukaci A Sa Dokar Ta-Baci A Jihohin Zamfara Da ...

Kashe-Ashe: An Bukaci A Sa Dokar Ta-Baci A Jihohin Zamfara Da Katsina Da Kaduna

271
0
PIC 14. CHIEF OF ARMY STAFF, LT.-GEN AZUBUIKE IHEJIRIKA, BEING RECEIVED BY THE FCTPOLICE COMMISSIONER, MR MICHAEL ZOUKUMOR, AT THE SCENE OF A BLAST THAT ROCKED UNHOUSE IN ABUJA ON FRIDAY (26/8/11).

An bukaci gwamnatin tarayya ta sanya dokar ta-baci a jihohin Zamfara da Kaduna da Katsina domin kawo karshen zubar da jini a jihohin.

Kiran ya fito ne daga bakin shugabannin kabilar Ijaw, da matasan kabilar Igbo.

Matsalar tsaro a jihohin Zamfara da Kaduna da Katsina da babu alamar ranar daina shi, ya sa shugaban kabilar Ijaw Cif Edwin Clarke da matasan kabilar Igbo, su ka ba gwamnatin tarayya shawarar cewa, hanya daya da za a bi domin kawo karshen matsalar tsaro a jihohin ita ce sanya dokar ta-baci.

Clark da shugaban matasan kabilar Igbo Okechukwu Isiguzoro, sun yarda cewa tunda matakin da gwamnati ta ke dauka na kawo karshen zubar da jini a jihohin bai yi aiki ba, su na ganin hanya daya da za a bi domin kawo karshen matsalar ita ce a hana mutane fita a yankunan da abin ya shafa.

Isiguzoro, ya ce babu wata ja-in-ja a zancen sanya dokar ta-baci a jihohin, saboda an kashe rayuka masu yawan gaske a jihohin, don haka dole ne gwamnatin tarayya ta sanya dokar ta-baci a jihohin ko da ta tsawon watanni uku ce.

Leave a Reply