Home Labaru Karancin Fetur: Kachikwu Ya Bayyana Dalilin Da Suka Janyo Wahalar Mai A...

Karancin Fetur: Kachikwu Ya Bayyana Dalilin Da Suka Janyo Wahalar Mai A Wasu Jihohi

241
0

Karamin ministan man fetur Ibe Kachikwu ya ce an samu dogayen layuka a gidajen man fetur da ke wasu jihohin Nijeriya ne sakamakon gibin da aka samu a jigilar man da ake yi, wanda hakan bai da wata nasaba da karancin man fetur.

Da ya ke zantawa da manema labarai a jihar Legas, ministan ya bukaci ‘yan Nijeriya su yi watsi da jita-jitar cewa, za a yi karin farashin man fetur jihohin kasar’nan.

Kachikwu ya bayyana haka ne a taron kasa da kasa da aka gudanar a kan man fetur da iskar gas da ya gudana a Legas, ya kara da cewa, babu wani lokaci da jagororin gwamnati su ka zauna suka yi magana a kan karin farashin man fetur da ake ta yayatawa.