Home Labaru Rikicin Sarauta: Hakimin Bebeji Ya Yi Murabus Daga Mukamin Sa

Rikicin Sarauta: Hakimin Bebeji Ya Yi Murabus Daga Mukamin Sa

580
0

Hakimin karamar hukumar Bebeji da ke jihar Kano Haruna Sanusi ya yi murabus daga mukamin sa, bisa dalilai na rashin lafiya da kuma sauyin tsarin masarauta da aka samu kwanan nan.

Hakimin, wanda ke rike da mukamin Dan Galadiman Kano, ya sanar da ajiye aikin sa ne a cikin wata wasika da ya aike wa Sakataren gwamnatin jihar Kano.

Idan dai ba a manta ba, a ranar 8 ga watan Mayu ne, gwamnan jihar Kano ya samar da sabbin masarautu hudu da manyan sarakuna a jihar, inda aka yi zargin cewa ya na so ya karya darajar Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ne. Sabbin Sarakunan da Ganduje ya nada kuwa sun hada da na Bichi Aminu Ado-Bayero, da na Rano Tafida Ila, da Gaya Ibrahim Abdulkadir, da kuma Ibrahim Abubakar ll, a Karaye.

Leave a Reply