Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ya jagoranci zaman majalisar zartarwa ta tarayya a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Kafin fara zaman majalisar, an yi shiru na minti daya domin girmama tsohon Ministan Noma Malami Buwai, wanda ya rasu kwanan nan ya na da shekaru 76.
Ministocin da su ka halarci taron, sun hada da na yada labarai da al’adu Lai Mohammed, da Ministan shari’a Abubakar Malami, da Ministar Kudi Zainab Ahmed, Ministan wutar lantarki Sale Mamman da kuma na Ayyuka da Gidaje Babatunde Fashola.
Sauran sun hada da Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha, da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban kasa Ibrahim Gambari, da kuma mai ba shugaban kasa shawara ta fuskar tsaro Babagana Monguno.