Home Labaru Maslaha: Kamfanin Twitter Ya Amince Ya Kafa Ofishi A Nijeriya – Lai...

Maslaha: Kamfanin Twitter Ya Amince Ya Kafa Ofishi A Nijeriya – Lai Mohammed

35
0

Ministan Yaɗa Labarai Lai Mohammed, ya ce akwai yiwuwar buɗe shafin Twitter a Nijeriya nan ba da jimawa ba, bayan kamfanin ya amince da sharuɗɗan da gwamnati ta gindaya ma shi.

Lai Mohammed ya bayyana haka ne, jim kaɗan bayan kammala taron Majalisar Zartarwa da aka yi ta yanar gizo, a ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo.

Da ya ke amsa tambayoyin manema labarai, Lai Mohammed ya ce an samu ci-gaba tsakanin gwamnati da kamfanin, biyo bayan ganawar da aka sha yi tsakanin bangarorin biyu.

Ya ce kamfaninTwitter ya yarda da mafi yawan sharuɗɗa gwamnati ta gindaya ma shi, ciki kuwa har da kafa ofishi a Nijeriya.

Sai dai kamfanin ya ce har sai nan da zuwa shekara ta 2022 zai iya kafa ofishin a Nijeriya.