Gwamnatin Tarayya, ta ce ta sanya tsauraran ka’idojin balaguro zuwa kasashen waje ne domin kare ‘yan Nijeriya daga kamuwa da cutar ta Korona.
Ministan Yada Labarai da Al’adu Lai Mohammed ya bayyana haka, yayin da ya ke zantawa da manema labarau a Abuja.
Ya ce an sa Nijeriya a matsayin kasa mai tsatstsauran ra’ayi dangane da ka’idojin tafiye-tafiye, ya na mai cewa matsayin gwamnati shi ne kare al’ummar ta daga yaduwar cutar.
Ministan ya kara da cewa, Nijeriya ta sanya wasu kasashe a jerin kasashe masu hadari, sakamakon bullar annobar Korona nau’in Delta.
Daga cikin kasashen da aka sanya wa takunkumin, Lai Mohammed ya ce akwai Afirka ta Kudu da Indiya da Brazil da kuma Turkiya.