Home Labaru Shugabanci Nagari: Kungiya Ta Karrama Dogara Da Lambar Girma A Abuja

Shugabanci Nagari: Kungiya Ta Karrama Dogara Da Lambar Girma A Abuja

253
0

Shugaban majalisar wakilai Yakubu Dogara, ya ce majalisar dokoki ta 8 a karkashin jagorancin sa ta ba gwamantin shugaba Muhammadu Buhari goyon bayan da ya kamata.

Dogara ya bayyana haka ne a Abuja, jim kadan bayan wata kungiya ta karramashi da lambar girma saboda jajircewar sa a kan jagoranci nagari a majalisar wakilai.

Shugaban kwamitin kula da al’adu da dabi’u na majalisar, wanda shi ya karbi lambar girman a madadin Dogara, ya ce tabbas Dogara ya cancanci a yaba ma shi bisa namijin kokarin da ya yi na rike majalisar tsawon shekaru hudu.

An dai karrama Dogara ne, sakamakon rashin bata lokaci wajen isar da kudurin saukaka kasuwanci ga ‘yan Nijeriya da sauran kudurorin da su ka je gaban majalisar sa, wanda da dama daga cikin su a yau dokar kasa ta aminta da su.

Bugu da kari, Dogara ya yaba wa majalisa ta 8, a matsayin wadda ta fi shahara a tarihin Nijeriya tun daga shekara ta 1960 zuwa yau.