Home Labaru Kiwon Lafiya Kiwon Lafiya: Abin Da Ya Sa Manyan Asibitocin Nijeriya Ba Su Aiki...

Kiwon Lafiya: Abin Da Ya Sa Manyan Asibitocin Nijeriya Ba Su Aiki Yadda Ya Kamata – Minista

811
0

Ministan lafiya Isaac Adewole, ya ce manyan asibitocin da su ka hada da asibitocin koyarwa na jami’o’i za su fara aiki yadda ya kamata a Nijeriya, idan gwamnati ta inganta asibitocin jihohi da cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko.

Adewole ya ce, bisa ga yadda tsarin ya ke, gwamnati ta gina manyan asibitoci ne domin duba cututtukan da su ka gagari asibitocin jihohi da cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko.

Ya ce kamata ya yi asibitocin jihohi da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko su duba kashi 70 cikin 100 na marasa lafiya, inda ya gagagre su sai a garzaya zuwa manyan asibitoci, amma yanzu haka kanannan asibitocin duk sun mutu kowa manyan ya ke zuwa.

Adewole ya cigaba da cewa, gwamnati za ta yi nasarar cimma burin ta na samar da kiwon lafiya ingantacce cikin sauki ne, idan ta inganta asibitocin jihohi da cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko.

Leave a Reply