Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar, ya bayyana dalilin da ya sa ya bukaci shugabar kotun daukaka kara Zainab Bulkachuwa ta yanje daga shari’ar zaben shugaban kasa.
Atiku da jam’iyyarsa PDP dai su na kalubalantar nasarar shugaba Muhammadu Buhari, kuma sun bukaci Zainab Bulkachuwa ta janye daga rukunin alkalan da za su yanke hukunci a kan karar, duk da cewa ita ce shugabar tawagar.
Jam’iyyar PDP da Atiku Abubakar, sun ce dalilin mika wannan bukata shi ne, alakar Zainab Bulkachuwa da wani jigon jam’iyyar APC, kuma zababben sanata mai wakiltar jihar Bauchi.
A jawabin sa, Atiku ya ce shi da lauyoyin sa ba su bukaci janyewar Bulkachuwa don su na kokwanto a kan halayen ta ko kwarewar ta ba.
Ya ce dalilin da ya sa lauyoyin shi su ka bukaci ta janye shi ne, kasancewar mijin ta zababben sanata ne a karkashin jam’iyyar APC, lamarin da su ke ganin ba za ta yi masu adalci ba.