Home Labaru Shugaban Kungiyar NATFORCE Ya Bukaci ‘Yan Najeriya Su Kasance Masu Bin Doka...

Shugaban Kungiyar NATFORCE Ya Bukaci ‘Yan Najeriya Su Kasance Masu Bin Doka Da Ka’Ida

86
0

A cigaba da bukukwan sallar Kirsimeti Shugaban kungiyar dakile bazuwar makamai ba bisa ka’ida ba wato NATFORCE Dr. Baba Muhammad ya mika sakon fatan alheri ga illahirin kiristocin Najeria dama na yankin kasashen Afirka ta yamma,

A cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar ta NATFORCE ya rabawa manema labarai a nan Abuja, ya bayyana cewar wannan lokaci ne na hadin kan Al’ummar Najeriya da nuna soyayya ga juna, tare da imanin cewar kalubalen tsaron da Najeriya ke ciki na dab da zama tarihi.

Sanarwar ta kara da cewar kudirin kafa kungiyar ta zama hukuma wanda yanzu haka yake mataki na karshe a majalisar kasa na dab da samun amincewa wanda kuma zai bada wata dama ta musamman na dakile yadda makamai barkatai suke karakaina a hannun jama’a ba bisa ka’ida ba wanada ke haifar da hare-haren ta’addanci a kasa.

Daga karshe ya bayyana gamsuwar sa kan yadda ake samun hadin kai a tsakanin hukumomin tsaro tare da yadda shugaban kasa Muhammadu ke aiki tukuru wajen ganin an inganta walwalar jami’an tsaro dake fadi tashin ganin an wanzar da ingantaccen zaman lafiya a Najeriya.