Rahotannin da ke fitowa daga kananan hukumomin Isa da Sabon Birni da Gwaronyo da wani yanki na Karamar Hukumar Shinkafi a Jihar Zamfara na nuna sojoji suna ci gaba fattatakar ’yan bindigar da suka addabi yankunan, inda aka kashe da dama daga cikin su aka jikkata wadan su, sannan wadan su suka tsere.
Sai dai wadansu mutanen yankin sun ce duk da suna da labarin harin da ake kai wa ’yan bindigar, har yanzu su ma suna kai hare-haren.
Bashir Altine Guyawa Isa ya ce sojoji sun shiga yankin Kamarawa da Tozai da Surudubu da gefen Take Tsaba, ya ce a yankin akwai abubuwa na karfafa gwiwa duk da babu tabbacin kama daya daga cikin jagororin ’yan bindigar.
Ya ce a yanzu dai Fada ake yi, ba a tsammanin samun nasarar da mutane suke bukata cikin kankanin lokaci, amma su da lamarin ya shafa kaitsaye suna da hujjojin sojoji sun shiga yankin.
Idan ba’a manta ba dai a makon day a gabata ne kasurgumin dan bindigar nan, Bello Turji ya rubuta wata wasika inda yake naman a yi sulhu a daina kai musu hari.
You must log in to post a comment.