Gwamnatin Senegal ta sanar da cewa za a gudanar da zaben shugaban kasa a ranar 24 ga watan nan na Maris.
Kasar dai ta rika fama da dambarwar siyasa tun da Shugaba Macky Sall ya dage zaben da ya kamata a yi a watan daya gabata na Fabarairu.
A wata sanarwa da majalisar ministocin ta fitar ta ce, Shugaban Jamhuriyar ya gaya wa majalisar ministoci cewa an tsayar da ranar Lahadi 24 ga watan Maris a matsayin ranar kada kuri’a.
Kafin sanarwar ta ranar Laraba, hukumomi sun yi kokarin dage ainahin ranar zaben ta 25 ga watan Fabarairu zuwa watan Disamba, abin da ya haddasa mummunar tarzoma a kasar.
To amma daga baya kotun kolin kasar ta zartar da cewa dole ne a gudanar da zaben kafin ranar 2 ga watan Afirilu.