Hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC, ta sake kama mutane biyu makusantan Atiku Abubakar na jam’iyyr PDP.

An dai tsare mai ba Atiku Abubakar shawara a kan lamarin doka Uyi Giwa Osagie, da kuma surukin sa Abdullahi Babalele da yammacin ranar Alhamis da ta gabata.
Wasu majiyoyi sun ce an kama mutanen biyu ne, bayan amsa gayyatar hukumar EFCC a jihar Lagas.
Rahotanni
sun ce hukumar EFCC ta na shirin gurfanar da Giwa-Osagie ne bisa zargin zambar
wasu kudade.














































