Home Labaru Shugaba Buhari Ya Yi Iyakar Bakin Kokarin Sa – Obasanjo

Shugaba Buhari Ya Yi Iyakar Bakin Kokarin Sa – Obasanjo

87
0

Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya sake jaddada matsayin sa na ci gaba da dorewar Najeriya a matsayin dunkulalliyar kasa sabanin ‘yadda wasu bangarori ke fafutukar ganin sun balle domin kafa kasa ta kan su.

Yayin da yake gabatar da jawabi a wajen wani taro da Cibiyar zaman lafiya ta shirya wanda ke karkashin Mai Alfarma Sarkin Musulmin Najeriya Muhammad Sa’ad Abubakar da tsohon shugaban kungiyar Kiristoci ta kasa Cardinal John Onayekan, Obasanjo yace ya zama wajibi kowanne ‘dan Najeriya ya bada gudumawar sa wajen tinkarar matsalolin da suka addabi Najeiya.

Tsohon shugaban kasan ya ce kuskure ne mutane su dinga rungume hannun su suna cewa babu ruwan su da abinda ke faruwa ko kuma suce abinda ke faruwa wata matsala ce ta wata shiya wadda bata shafe su ba.

Obasanjo yace a matsayin sa na ‘dan kabilar Yarbawa ba zai taba goyan bayan kafa kasar Yarbawa zalla ba, domin kuwa shi ya amince da ci gaba da zaman Najeriya a matsayin kasa guda.

Tsohon shugaban yace bai taba amfani da kabilar sa wajen neman biyan bukata a Najeriya ba, saboda shi ya amince da cewar Najeriya ta fi karfin kowacce kabila ko addini ko kuma shiya.

Obasanjo yace shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi iya bakin kokarin sa, kuma abinda yake yi yanzu shine mayar da hankali akan shugabancin da za’a samu bayan shi, wanda ake saran ya dora daga inda ya tsaya.