Home Labaru An Kashe Mutum Tara Da Raunata Biyu A Sassan Kaduna

An Kashe Mutum Tara Da Raunata Biyu A Sassan Kaduna

62
0

Gwamnatin Jihar Kaduna ta bayyana cewa ƴan bindiga sun kashe mutane tara da kuma raunata mutum biyu a wasu hare-haren da aka kai a Ƙananan Hukumomin Chikun da Zariya da kuma Zangon Kataf.

A wata sanarwa da kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Samuel Aruwan ya fitar, ya ce an kashe mutum uku yayin da ƴan bindiga suka yi wa garuruwan Buruku da Udawa tsinke.

Haka kuma a yankunan Yola da Kadi da ke Ƙaramar Hukumar Chikun, ƴan bindigar sun kashe mutum guda da raunata ɗaya.

Ya kara da cewa ‘yan bindigan sun sake kashe mutum biyu a ƙauyen Sako da ke Zangon Kataf, haka kuma an gano gawarwakin mutum biyu a yankunan Kurfi da Magamiya da ke Zangon Kataf ɗin.

Haka ma a Ƙaramar Hukumar Zaria, an kashe mutum ɗaya a ƙauye Saye.

Gwamnan jihar Kaduna,  Malam Nasir El-Rufai ya nuna ɓacin ran sa kan wannan lamari tare da addu’a ga waɗanda suka rasu da kuma waɗanda suka jikkata su samu sauƙi.